Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da wata sanarwar da hukumar kare muhallin ta MDD ta fitar ke cewa, kasashe sama da 20 sun nuna goyon bayansu ga gangamin na Clean Seas, wanda ke kira ga gwamnatoci da masana'antu da daidaikun mutane su kawo karshen amfani da kayayyakin roba sau daya da kuma daina sanya sinadaran roba cikin kayan kwalliya, wadanda su ne jigo wajen gurbata tekuna, kawo shekarar 2022. (Fa'iza Mustapha)