Mataimakin Daraktan hukumar kula da sha'anin teku na kasar Sin Lin Shanqing, wanda ya bayyana haka yayin zaman taron a jiya Laraba, ya ce akwai bukatar al'ummomin kasashen waje su inganta hadin kai wajen kare tekuna.
Lin Shanqing, ya ce la'akari da matakan da ta bi wajen samun ci gaba, a shirye kasar Sin take ta taka muhimmiyar rawa wajen kulla ingantacciyya hadin gwiwa mai karfi da sauran kasashe da hukumomin ta yadda za a mori juna wajen kare gurbatar teku.
Taron na MDD kan kare teku na gudana ne a hedkwatar majalisar dake birnin New York, daga 5 zuwa 9 ga watan Yuni, inda ranar kare Teku ta duniya wato 8 ga watan Yuni za ta fada cikin ranakun da ake taron.
Mataimakin Daraktan ya bayyanawa taron cewa, kasar Sin ta dauki matakan kare muhallin halittun cikin teku.
Ya ce an shata wasu yankunan halittun teku, inda karkashinsa, aka kebe wasu yankunan masu matukar muhimmanci da ake sa ido sosai kan abubuwa dake gudana a wuraren. (Fa'iza Mustapha)