Taron samar da makamashin na WACEC, na daya daga cikin jerin abubuwan da za'a gudanar a bikin makon na Afrika a wannan karo, ana daukarsa a matsayin wani sa kaimi ne ga gwamnatoci da hukumomin samar da makamashi, da su tashi tsaye wajen sauke nauyin dake kansu na bullo da hanyoyin samar da makamashi domin samun moriyar dunbun al'ummomin dake shiyyar.
Manufar shirin dai shi ne, yunkurin kara samar da makamashi da kashi 88 bisa 100 ga al'ummomin shiyyar yammacin Afrika nan da shekarar 2030, kamar yadda Jansénio Delgado, wani kwararre a fannin samar da makamashi marar gurbata muhalli na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS a cibiyar samar da makamashi marar illa ga muhalli da inganci wato (ECREEE) ya tabbatar da haka.
Delgado ya shedawa wakilan mahalarta taron cewa kashi 52 bisa 100 na al'ummomin dake shiyyar yammacin Afrika ba su da hasken lantarki.
Shiyyar yammacin Afrika tana da hanyoyi masu yawa na samar da makamashi marar illa ga muhalli da suka hada da ruwa, hasken rana, iska, da kuma ta hanyar tsirrai. (Ahmad Fagam)