Cikin wani sabon rahoto da babban bankin duniyar ya fitar game da tattalin arzikin duniyar, ya yi hasashen cewa a shekarar 2018 mai zuwa, tattalin arzikin Sin zai karu da 6.3, daidai da hasashen da bankin ya riga ya yi tun a watan Yunin shekarar 2016.
Tsarin tattalin arziki na cikin gida da kasar ke amfani da shi a cewar rahoton, zai ci gaba da tallafawa manufofin kasar na raya tattalin arziki, duk kuwa da raguwar bukatar hajojin kasar a waje, da ma sarrafa hajojin da suka haura bukatar kasuwanni.
Kaza lika rahoton ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da samun ci gaba madaidaici kuma mai dorewa a matsakaicin mataki, yayin da take kaucewa mummunan koma baya. Hakan a cewar rahoton zai samar da nasarar da ake fata, idan har kasar ta ci gaba da gudanar da sauye sauye ga tsarin kashe kudade, da sauya fasalin kamfanoni ko hukumomi mallakar gwamnati, da kuma kwaskwarima ga kasuwar filaye da ta kwadago. (Saminu Hassan)