in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba da rawar da Sin ta taka wajen raya nahiyar Afirka
2017-06-19 09:36:33 cri

Wakilin hukumar raya masana'tun ta MDD (UNIDO) mai kula da kasashen Kenya, da Eritrea da Sudan ta kudu Emmanuel Kalenzi ya yaba da irin rawar da kasar Sin ta taka wajen raya nahiyar Afirka.

Jami'in na MDD wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabin a taron harkokin zuba jari da aka kammala ba da dadewa ba a birnin Shenzhen dake nan kasar Sin, ya ce gagarumar rawar da mahukuntan kasar ta Sin ke takawa a nahiyar ta Afirka ta taimaka matuka wajen farfado da harkokin tattalin arzikin nahiyar.

Kalenzi ya ce, an gina hadin gwiwar Sin da Afirka ce bisa tushen mutunta juna da cin moriyar juna. Kuma har yanzu akwai tarin damammaki da muhimmiyar rawar da Sin din za ta taka wajen bunkasa nahiyar ta Afirka. Duba da fifikon da kasar ta Sin ke da shi kan nahiyar ta Afirka a fannonin kere-kere da sauran fasohohi.

Jami'in ya ce mahukuntan na Sin suna kuma maraba da shugabannin nahiyar Afirka wadanda ke da aniyyar kullar huldar cinikayya maimakon ba da tallafi kadai ga nahiyar.

A watan Disamban shekarar 2015 ne UNIDO ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar raya harkokin cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin, ta yadda sassan biyu za su yi hadin gwiwa wajen bunkasa harkokin cinikayya da zuba jari a kasashe masu tasowa.

Bayanai na nuna cewa, kasar Sin ce ke kan gaba wajen zuba jari a nahiyar ta Afirka, baya ga samar da guraben ayyukan yi a nahiyar ta Afirka da kamfanonin kasar da suka zuba jari a nahiyar suka yi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China