Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao, ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan kasashen dake kahon nahiyar Afirka wato yankin arewa maso gabashin Afirka, za su kara yaukaka dankon zumunci da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu, domin ganin an warware sabani ta hanyar tattaunawa, tare da dakile ayyukan ta'addanci, domin moriyar yankin baki daya.
Yayin taron da kwamitin sulhun MDD ya shirya a jiya, domin tattauna aikin kwamitin sanya takunkumi kan Somaliya da Eritrea, Wu Haitao ya bayyana cewa, yankin kahon Afirka yana da muhimmanci matuka, kuma kasashen dake yankin su na kokarin samun ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya.
Wu wanda ya ce, sanya takunkumi ba mafita ba ce, mataki ne da ake dauka yayin da ake kokarin warware matsala ta hanyar siyasa, ya yi fatan kwamitin sanya takunkumin zai gudanar da aikinsa bisa kudurin kwamitin sulhun.(Jamila)