Wakilai daga kasar Sin da na wasu kasashen Afirka, sun gudanar da taron ministocin lafiya a jiya Litinin a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu, domin bunkasa hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya.
Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, da minista a ma'aikatar lafiyar kasar Li Bin, da ministocin lafiya na kasashen Afirka 31, na cikin mahalarta taron wanda aka yiwa lakabi da "hadin gwiwar Sin da Afirka, daga tsarawa zuwa aiwatarwa."
Da take jawabi gaban mahalarta taron, Liu Yandong ta ce, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, jigo ne ga ci gaban makomar al'ummun sassan biyu.
Liu ta kara da cewa, an samu gagarumar nasara a fannin hadin kai ta fuskar musaya, da kawance tsakanin bangarorin biyu.
Yayin taron, wakilan kasar Sin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin magance mace macen yara, da mata masu juna biyu da wakilan kasar Malawi, da ta hadin gwiwar bunkasa asibitoci da kasashen Congo, da Ghana, da Mauritania, da Zambia, da Nijar da kuma Chadi.
A hannu guda kuma, sassan biyu sun amince da gudanar da aikin tiyatar hakiyar idanu a wasu kasashen Afirka da suka hada da kasar Saliyo.(Saminu)