in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Tecno na Sin ya yi cinikin miliyoyin wayar hannu a Afrika
2017-05-10 09:57:03 cri

Kamfanin kera wayar hannu na kasar Sin Tecno ya ce, ya sayar da wayoyin hannu miliyan 25, ciki har da wayoyin zamani wato smartphones miliyan 9 a shekarar 2015, hakan ya ba shi damar samun fiffiko mafi yawa a Afrika.

A shekarar bara kadai, kamfanin ya sayar da wayoyin hannun kimanin miliyan 60, yayin da adadin wayoyin zamanin da kamfani ya sayar ya karu da kashi 40 cikin 100. Kamfanin yana kuma kera na'urar tablets ga kasuwannin tsakiya da manyan kasuwanni.

Kamfanin ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a lokacin da kamfanin ya sanar da kaddamar da sabuwar wayar zamani da ya kera samfurin Camon X.

A yau Laraba 10 ga watan Mayu ne za'a kaddamar da sabuwar wayar ta kamfanin Tecno, kana za'a sayar da wayoyin a kasashen Afrika 41, da yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Latin Amurka bayan an kara inganta ta.

Mohammed Hasseni shi ne manajan kasuwanci na kamfanin wayar Tecno a kasar Habasha, ya ce, kashi 25 cikin 100 na kasuwannin wayoyin Afrika za su yi hada hadar wayoyin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China