Wannan rahoto na zuwa ne bayan da aka kimanta halin da maza da mata daga kasashe 144 suke ciki a bangaren samun guraben aikin yi, da damar samun ilmi, da gudanar da 'yancinsu na siyasa, da batun da ya shafi lafiyar jikinsu da yadda suke tafiyar da harkokinsu na rayuwa, bisa la'akari da suke cin gajiyar albarkatu da sauran damammaki.
Sai dai kuma rahoton ya nuna cewa, ba a fuskantar bambancin jinsi sosai a kasashen da ke yammacin Turai, amma kuma kasashen Afirka hudu da ke yankin kudu da hamadar Sahara na cikin jerin kasashe 20 da ke sahun gaba, wadanda suka hada da kasashen Ruwanda, Burundi, Namibia da kuma Afirka da Kudu. Rahoton ya ce, akwai babban gibi na rashin daidaito a tsakanin maza da mata a yankin gabas ta tsakiya da kuma yankin arewacin nahiyar Afirka.(Kande Gao)