An fitar da "shirin tinkarar matsalolin kiwon lafiya da suka faru ba zato" bayan da aka sha darussan aukuwar annobar Ebola a yankin yammacin Afirka. Wannan ya nuna cewa, za a gyara matsayin da kungiyar WHO take dauka, wato ba ma kawai za ta ci gaba da yin amfani da fasahohin da ake amfani da su yanzu kamar yadda ya kamata ba, har ma za a kara karfinta na tinkarar annobar da za ta auku ba zato da na samar da tallafin jin kai cikin sauri.
A cikin jawabinta na rufe taron, Madam Margaret Chan, babbar direktar kungiyar WHO ta bayyana cewa, sabon shirin da aka tsara ya bullo da wata alamar siyasa da gangan, kungiyar ta kasance wata kungiyar da ake amincewa da ita sosai a duk fadin duniya a fannin kiwon lafiya, kungiyar za ta ci gaba da shugabanta da kuma daidaita matakan tinkarar matsalolin kiwon lafiya da za su faru ba zato a nan gaba. (Sanusi Chen)