Daraktar ofishin UNESCO a yankin gabashin Afrika, Ann Therese Ndong-Jatta, ta ce tallafin da kasar Sin ke ba bangaren ilimi a Afrika na taimakawa wajen horar da malamai, al'amarin da ta bayyana a matsayin muhimmin batu wajen horas da al'umma domin samun ci gaba.
Ann Therese Ndong-Jatta ta bayyana haka ne yayin da take ganawa da manema labarai, inda ta jinjinawa tallafin da kasar Sin ke badawa ga bangaren ilimi a nahiyar Afrika cikin shekaru da dama.
Kasar Sin ta hannun hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO, ta ba da gudunmuwar kayayyaki ga cibiyoyin horas da malamai guda uku dake kasar Uganda a ranar 3 ga watan nan.
Kididdigar ofishin jakadancin kasar Sin ta bayyana cewa, malamai 137 ne aka horar tare da ba da gudunmuwar kayayyakin fasahar sadarwa har guda 272.
Ann Ndong-Jatta ta ce, an horar da malamai yadda za su shigar da fasahar zamani cikin tsohon tsarin koyarwa.
Haka zalika, Sin din ta hannu UNESCO na aiwatar da wani shiri na dalar miliyan 8 dake da nufin cike gibin dake akwai a bangaren ilimi a nahiyar
Shirin na shekaru hudu da aka fara a shekarar 2012 na mai da hankali ne kan samar da isasshen adadin kwararrun malamai a nahiyar ta hanyar horarwa.
Kasashen nahiyar 8 da suka hada da Cote d'Ivoire, da Habasha, da Namibia, da Jamhuriyar Demokraddiyar Congo, da Congo, da Liberia, da Tanzania, da kuma Uganda ne ke cin gajiyar shirin. (Fa'iza Mustapha)