Da take jawabi a bikin bude taron, shugabar hukumar zartaswar kungiyar Nkosazana Dlamini-Zuma, ta yaba da nasarar da aka samu, a fannonin da suka shafi sufuri cikin 'yanci, da ingantar sufurin jiragen kasa, da kuma dakile yiwa yara kanana aure.
Uwar gida Zuma ta jinjinawa bunkasar tattalin arzikin wasu kasashen Afirka da suka hada da Habasha, da jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, da Cote d'Ivoire, da Mozambique, da Tanzania, da kuma Rwanda. Kasashen da aka yi amannar suna kan gaba wajen samun ci gaba a duniya.
Kaza lika Zuma ta yabawa wasu kasashen Afirka 13, da suka bude kofar su ga sauran kasashen Afirka, a fannin cin gajiyar shirin nahiyar na fadada kasuwar sufurin jiragen sama a wannan shekara ta 2017.
Har wa yau ta nuna farin ciki, game da ci gaba da aka samu a fannin samar da daidaiton jinsi, da inganta rayuwar mata, da kara yawan damar su a fannonin wakilcin al'umma. Sai kuma fannin rage mace macen mata masu juna biyu, da yara kanana, da dai makamantansu.
A daya bangaren kuma, uwar gida Zuma ta nuna rashin jin dadin ta, game da ta'azzarar rikici a Sudan ta Kudu, tana mai fatan sassan da rikicin ya shafa, za su martaba yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu, tare da rungumar matakan adalci.