Kaza lika an rantsar da jami'ai da za su kula da harkokin wanzar da zaman lafiya, da tsaro, da sashen siyasa. Sai kuma na hada hadar cinikayya, da jin dadin jama'a. Kana akwai jami'an lura da samar da ababen more rayuwar jama'a, da makamashi, da raya karkara, da fannin tattalin arziki da kuma bunkasa noma.
Taron AU na 28 da ya kammala a jiya Talata, ya kuma zabi shugaban kasar Guinea Alpha Conde, a matsayin shugaban kungiyar na karba karba.
Da take jawabin ban kwana da mahalarta taron, tsohuwar shugabar hukumar zartaswar AU uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana taron a matsayin wanda ya cimma nasarori da dama, wadanda za su amfani al'ummun nahiyar Afirka baki daya.
A nasa bangaren, sabon shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat, ya ce a shirye yake ya hada kai da sauran masu ruwa da tsaki, wajen aiki tukuru domin cimma nasarar kudurorin da kungiyar ta sanya gaba. (Saminu)