Yayin taron na jiya da ya gudana karkashin Ministar harkokin wajen Rwanda Louse Mushikiwabo, kwamitin sulhun na AU, ya tafka muhawara kan batutuwa biyu; da suka hada da zirga-zirgar mutane da safarar kayayyaki ba tare da wani tsaiko ba a nahiyar Afrika, da kuma kare yara daga shiga rikice-rikice musammam batun mai da su sojoji yayin da ake yaki.
A jawabinta na bude taron, Mushikiwabo ta ce da yawa daga cikin wadanda ke fada a rikicie-rikicen Afrika yara ne, inda ta ce an kiyasin cewa, kashi arba'in na yara sojoji 'yan Afrika ne, ta na mai cewa ba za a lamunci hakan ba, domin kamata ya yi a ce suna makarantu maimakon kasancewa a bakin daga.
A nasa jawabin, Daraktan kwamitin, Admore Kambudzi, ya ce akwai bukatar kara ba batun kare yara daga shiga rikici muhimmanci, musammam batun yara sojoji, a kokarin cimma muradin ajiye makami da kungiyar AU ke son cimmawa nan da shekarar 2020. ( Fa'iza Mustapha)