Wakilan kasar Sin da na Afirka ta kudu, sun kaddamar da wani dandali na hadin gwiwa a fannin kimiyya, a wani mataki na karfafa hadin kai wajen raya harkokin kimiyya da fasaha tsakanin kasashen biyu.
Da yake jawabi yayin kaddamar da dandalin a jiya Litinin, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, ta ce an cimma gagarumar nasara game da hadin gwiwar Sin da Afirka ta kudu a fannin bunkasa kimiyya da fasaha, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin sassan 2 shekaru kusan shekaru 20 da suka gabata.
Ta ce, fannonin da kasashen biyu suka maida hankali kan su sun hada da nazarin kimiyyar halittu, da na fasahar sadarwa, da hakar ma'adanai, da samar da sabbin kayayyaki, wanda hakan ke nuna irin muhimmanci da sassan biyu ke baiwa harkokin kimiyya da fasaha.
A watan Disambar shekarar 2014 ne dai shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaran sa na Afirka ta kudu Jacob Zuma, suka cimma matsaya, game da kafa dandalin na kimiyya cikin hadin gwiwa. Yayin taron su na farko game da fadada musaya tsakanin al'ummun kasashen biyu ko (PPEM) a takaice wanda ya gudana a jiyan, wakilan sassan biyu, sun sanya batun musaya a fannin kimiyya da fasaha, cikin fannonin hadin giwar su a nan gaba.(Saminu)