Bisa gayyatar da majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu ta yi masa, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC Qiangba Puncog ya yi ganawa da shugaban kwamitin harkokin jihohin kasar Afirka ta Kudu Modise a birnin Cape Town jiya Talata, kuma ya jagoranci taro karo na hudu da aka gudana kan tsarin cudanya dake tsakanin hukumomin tsara dokoki na Sin da Afirka ta Kudu tare da mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar ta Afirka ta Kudu.
Qiangba Puncog ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, Sin da Afirka ta Kudu suna tafiyar da huldar dake tsakaninsu yadda ya kamata, hadin gwiwa da cudanya dake tsakanin hukumomin tsara dokoki na kasashen biyu su ma suna kara karfafuwa, a bayyane ne sassan biyu suna kokarin kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin su bisa tushen matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sakamakon da aka samu a yayin taron kolin Johnnesburg na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kana suna kokarin yin cudanya wajen tafiyar da harkokin kasashen su domin kara ciyar da huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu gaba
A nata bangare kuma, Afirka ta Kudu ta yaba wa huldar dake tsakanin sassan sosai, kuma ta jaddada cewa, tana son sanya kokari tare da kasar Sin domin kara samun fahimtar juna a fannin siyasa, da kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu, tare kuma da kara kyautata hadin gwiwa da cudanya dake tsakanin hukumomin tsara dokoki na kasashen biyu, da haka za a sa kaimi kan ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, da kuma Sin da kasashen Afirka gaba yadda ya kamata.(Jamila)