Gwamnatin Afrika ta Kudu ta sanar a ranar Laraba cewa, dangantakarta tare da kasar Sin za ta tsaya wa mai muhimmanci domin cimma tsarinta na bunkasuwa. Wannan hulda za ta baiwa kasashen biyu damar yin hadin gwiwa da aiki tare a wasu fannoni da suka hada da noma, batutuwan muhalli, kasuwanci, masana'antu da kudi, a lokacin da kuma Afrika ta Kudu take ci gaba da aiwatar da shirinta na bunkasuwa, in ji gwamnatin kasar a cikin wata sanarwa da aka fitar a albarkacin ziyarar aiki ta shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Afrika ta Kudu. Haka kuma, wannan ziyara wata dama ce ta bitar dukkan nasarorin da aka samu a fannonin yin musanya da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, da ma kuma fadada da kuma tsara wasu sabbin fannonin dangantaka. (Maman Ada)