Ministan yawon bude ido na kasar Afrika ta Kudu Derek Hanekom ya ce, yawan masu yawon bude ido daga kasar Sin zuwa Afrika ta Kudun ya ninka sau daya da rabi a watan Janairun bana idan aka kwatanta da watan Janairun shekarar 2015.
Hanekom ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa a lokacin mikawa majalisar dokokin kasar kasafin kudi.
Domin tabbatar da samun karuwar masu zuwa yawon bude ido a kasar, a kwanan nan ministan ya ziyarci kasashen Sin da Indiya wadanda su ne manyan abokan huldar kasuwanci na kasar Afrika ta Kudun.
Hanekom ya ce, a kasar Sin sun samu gagarumar nasara game da ba da dama ga kamfanonin dake samar da takardun izinin shiga kasar a madadin masu tafiye tafiyen.
Ya ce, wannan na daga cikin yunkurin da Afrika ta Kudun ke yi na sassauta dokokin da suka shafi neman takardun izinin shiga kasar, sabanin a lokacin baya inda ake fuskantar wahalhalu game da samun takardun izinin.
Hanekom ya ce, harkokin kasuwancin kasar Sin suna kara samun bunkasuwa, kuma akwai alamun zai ci gaba da samun tagomashi.(Ahmad Fagam)