Ma'aikatar harkokin kudin Amurka, ta ce babu wata abokiyar cinikayyar Amurka, ciki har da kasar Sin, dake magudi wajen hada-hadar kudadenta, sai dai akwai wasu jerin kasashen shida da ta sanya wa ido, la'akari da cewa, ka'idojin sauyin kudadensu na bukatar a sa musu ido.
Yayin da take gabatar da rahotonta na rabin shekara ga majalisar dokoki kasar kan tattalin arzikin duniya da ka'idojin musayar kudaden ketare, ma'aikatar ta ce, babu wata muhimmiyar abokiyar cinikayyar Amurka ciki har da Kasar Sin da ta yi magudi kan takardar kudinta, don ci gaba da rage mata daraja fiye da kima.
Sai dai, ta sanya kasar Sin da yankinta na Taiwan, da kasashen Japan da Korea ta Arewa da Jamus da Switzerland cikin jerin wadanda ake sawa ido, tana mai cewa, akwai bukatar a rika bibiyar ka'idojin musayar kudadensu.
Rahoton ya ce kasar Sin ta kasance cikin jerin kasashen ne saboda rashin daidaito bisa tasirinta a gibin kudaden cinikayyar Amurka, duk da cewa rarar kudaden alkaluman tattalin arzikinta ya sauka zuwa kashi 1.8 a bara, wanda ya sauka idan aka kwatanta da kashi 2.8 da yake a shekarar 2015.
A cikin wannan makon ne yayin wata tattaunawa, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce cikin watanni, kasar Sin ba ta magudi kan kudadenta, wannan dai a mai da lashewa ne, idan aka yi la'akari da jawaban da ya rika yi lokacin da yake yakin neman zabe. (Fa'iza Mustapha)