Binciken da Gallup ya yi tsakanin ranakun 1 zuwa 5 na wannan watan, ya nuna cewa, adadin al'ummar Amurka dake yi yawa Sin kyakkyawar fahimta ya haura daga kashi 44 a bara, da kuma kashi 41 a shekarar 2012.
An samu karuwar kashi shidan ne a tsakanin 'yayan jam'iyyar Democrat da na Republican baki daya.
A kan samu wasu matsaloli kan huldar dake tsakanin kasashen Amurka da Sin cikin shekaru da dama da suka wuce, saboda batutuwa da suka shafi yankin Taiwan da Makamin Nukiliya da hakkin dan Adam da sauransu. Kuma zaben dan jam'iyyar Republican Donald Trump a matsayin shugaban Amurka ya kara dagula lissafi.
Duk da ba a san makomar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba, abu ne mai muhimmanci sabuwar Gwamnatin kasar Amurka ta san cewa, a yanzu Amurkawa ba sa ganin kasar Sin a matsayin barazana, al'amarin da zai taimaka wajen saukaka al'amura a dangantakar kasashen biyu, in ji kamfanin Gallup. ( Fa'iza Mustapha)