A wata hira da yayi da jaridar Wall Street Journal, Trump yace kasar Sin bata da hannu wajen yin zagon kasa ga sha'anin kudaden.
A lokacin yakin neman zabensa Trump, ya sha zargin kasar Sin da yin baba kere game da sha'anin kudadenta saboda rage darajar kudinta domin samun karuwar fitar da kayayyakinta ketare, sai dai masana tattalinn arziki na ganin cewar darajar kudin kasar Sin RMB yana tsaye ne cik a 'yan shekarun da suka gabata.
A shekarar 2015, asusun bada lamini na kasa da kasa IMF, ya ayyana cewa darajar kudin kasar Sin baya raguwa.
A tattaunawar, Trump yayi korafin cewa darajar dalar Amurta tayi mummunan karfi. Amma yace hakan kuskurensa ne saboda mutane sun bashi amanna. Wannan abune mai ciwo matuka, inji mista Trump.