in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Kenya miliyan 2.7 na bukatar taimakon abinci
2017-02-07 09:45:04 cri

Fari ya yi sanadin da adadin jama'ar kasar Kenya dake neman taimakon abinci ya tashi daga miliyan 1.3 a cikin watan Agustan bara, zuwa miliyan 2.7 cikin watan Junairun da ya gabata.

Hukumar tunkarar annoba ta kasar ce ta fitar da wani rahoto jiya, inda ta ce, galibin mutanen da abun ya shafa tsoffi ne da marasa lafiya da iyaye mata da yara 'yan kasa da shekaru biyar.

Hukumar ta ce, adadin shi ne kusan kashi ashirin cikin dari na wadanda ke zaune a yankunan makiyaya, kashi 18 kuma na yankunan marasa galihu, inda ta kara da cewa, matsalar na kara ta'azzara a wasu yankunan kasar.

Mataimakin shugaban kasar William Ruto ya ce, gwamnati ta fitar da dalar Amurka miliyan 16, domin sayan kayayyakin abinci daban-daban da za a raba a yankunan da abun ya shafa.

Ya kuma musanta ikirarin da ake cewa, gwamnati ta shigar da masara kasar daga ketare domin magance matsalar, maimakon ta saya a cikin gida. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China