Kwararru kan harkar samar da abinci sun yi kira ga kasashen nahiyar Afirka da ke kudu da hamadar Sahara da su inganta manufofinsu, tare da kara zuba jari a bangaren aikin gona.
Wannan kira na kunshe ne cikin wani rahoto da kwararru kan samar da abinci suka fitar a jiya Alhamis, wadda ke jaddada bukatar inganta tsare-tsaren samar da abinci, maimakon inganta hanyoyin kudaden shiga da jama'a ke samu.
Rahoton na wannan shekara da kungiyar da ke nazari kan alkaluman tsaron abinci na duniya (GFSI) ta saba fitarwa ko wace shekara, wadda sashen bincike kan yanayin tattalin arziki na kasa da kasa (EIU) ya fitar a birnin Nairobi na kasar Kenya, ya nuna cewa, kusan an samu kyautatuwar yadda ake samar da abinci a ko wace shiyya ta duniya cikin 'yan shekarun da suka gabata.
Darektan shiyya na Dupont mai kula da kasashen nahiyar Afirka da ke kudu da hamadar Sahara Richard Okine ya ce, akwai bambanci sosai a dangane da kalubalen da kasashen da suka ci gaba da kasashe masu tasowa ke fuskanta wajen samar da abinci.
A cewarsa, babbar matsalar da ke damun kasashe masu tasowa ita ce kayayyakin more rayuwa, ciki har da wuraren adana abinci, hanyoyi da tashoshin jiragen ruwa, sama da na kasa da karancin kudaden shiga daga mazauna da kuma rashin abinci masu gina jiki.(Ibrahim)