Jami'in MDD dake shugabantar ofishin tsare-tsare, na shirin lura da sauyin yanayi a nahiyar Afirka Richard Munang, ya bayyana bukatar sauya tsarin da nahiyar Afirka ke bi don amfana daga noma.
Munang ya ce, kamata ya yi shugabannin nahiyar su gaggauta sauya manufofinsu a fannin noma, ta yadda wannan sana'a za ta zamo hanyar habaka kasuwanci, da cinikayya, tare da samar da arziki ga al'ummar Afirka.
Jami'in ya kara da cewa, shigar da mata da matasa cikin tsare-tsaren bunkasa noma, zai taimaka matuka wajen fadada ribar da ake samu daga sana'ar.
A cewarsa, kaso 65 bisa dari na kasar noma da ake da ita a nahiyar, ta isa ta samar da isasshen abinci, tare da guraben ayyukan yi ga kaso 60 bisa dari na matasa marasa ayyukan yi a nahiyar.
Ya kuma bayyana rashin baiwa matasa damar mallakar filayen noma a nahiyar, a matsayin daya daga dalilan dake hana su damar samun basussukan banki na inganta sana'ar ta noma. Don haka ya yi kira da a samar da hanyoyin karfafa kwarewa, da na samar da horo, da dukkanin tallafin da ya dace domin cimma wannan buri na bunkasa noma.
Daga nan sai Mr. Munang ya bukaci jami'o'i da su shigar da darussan koyar da sana'o'i cikin manhajojin karatun daliban su, ta yadda hakan zai tallafawa ci gaban sana'ar noma tsakankanin dalibai masu kammala karatu. A cewarsa, dalibai kimanin miliyan 17 ne ka iya samun ayyukan yi a fannin aikin gona a duk shekara, muddin dai an inganta tsarin kasuwanci, da samar da bashi ga sashen ayyukan noma.(Saminu)