Masanan kimiyyar abinci mai gina jiki sun yi wani taro a ranar Talatan nan tare da yin kira ga kasashen nahiyar Afirka da su dauki matakan da suka dace domin shawo kan matsalar karin abinci mai gina jiki a wajen yara.
Shugabar kungiyar masanan abinci mai gina jiki ta Afrika Joyce Kinabo ta ce, rashin abinci mai gina jiki a wajen yara a Afrika har yanzu ya zama babban kalubale da ke bukatar daukan matakin don magance shi. Joyce Kinabo ta bayyana cewa, hakan ya wajaba idan aka yi la'akari da cewa, yawancin kasashe a nahiyar suna samar da wadataccen abinci a duk shekara.
Dr Joyce Kinabo da take jawabi a gaban mahalarta taron karo na 3 da ya samu mahalarta sama da 1,000 daga kasashen Afrika da sauran kasashen duniya, ta ce, bincike ya nuna cewa, karancin abinci mai gina jiki shi ne silar mutuwar yara kanana da kashi 1 bisa 3 a fadin nahiyar, duk da cewar yawancin kasashen dake kudu da Sahara na dogara ne a kan amfanin gona.
Dr Kinabo ta bukaci al'umma da su karfafa gwiwwar ganin an samar da abinci mai gina jiki a nahiyar, sannan ya kuma zama abin da zai sa a kara nazari da daukan matakai na yaki da duk wani nau'in karancin hakan.
A cewar Dr Joyce Kinabo, a cikin 'yan shekarun nan, yankin Afrika dake kudu da Sahara ya fuskanci yake yake da dama inda mata da yara kanana ke fadawa cikin mawuyacin hali, abin da ya sa kungiyar ke shawartar bukatar da ke akwai ga shugabannin kasashen Afrika da su fuskanci wannan kalubale ta hanyar tabbatar da an dakatar da yake yake a nahiyar. (Fatimah)