Bankin Duniya ya sanar a jiya Lahadi cewa, zai samar wa kasashen Afirka da ke kudu da Hamadar Sahama dala biliyan 57, don goyon bayan ci gaban nahiyar.
Shugaban Bankin Duniya Jim Yong, ya yi wannan tsokaci ne cikin sanarwar da aka fitar, bayan kammalar taron ministocin kudi da shugabannin babban banki na kasashen G20, wanda ya gudana a birnin Baden-Baden na kasar Jamus, inda ya kara da cewa, za a kaddamar da wannan taimako ne daga watan Yuli na bana. Kaza lika za a yi mafani da kudin ne a fannonin ilmi, da raya aikin gona, da kiwon lafiya, da ma samar da muhimman ababen more rayuwa.(Kande Gao)