in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya kaddamar da shirin inganta rayuwar 'yan gudun hijira a Sudan
2016-12-19 09:52:43 cri

Bankin duniya ya kaddamar da kashi na biyu na shirin samar da dawwamamman ci gaban rayuwar mutanen da rikici ya raba da matsugunansu (SLDP) a jahar Kassala dake gabashin kasar Sudan.

Wakilin bankin duniya a Sudan, Xavier Furtado, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa, shirin zai samarwa al'ummomin yankunan da rikici ya jefa rayuwarsu cikin garari hanyoyin da za su iya samarwa kansu sana'o'in dogara da kai.

Ya ce, kashin biyu na shirin za'a kashe kimanin dala miliyan 4.4, ya kara da cewa, idan aka inganta rayuwar al'ummomin da rikicin ya shafa, zai rage musu radadin halin damuwa da suka shiga a sanadiyyar barin muhallan nasu.

A watan Oktoban shekarar 2013 ne aka kaddamar da kashin farko na shirin, kuma aka karkareshi a watan Maris na wannan shekara, inda aka kashe dalar Amurka miliyan 3, wanda asusun bunkasa zaman lafiya da ci gaba na bankin duniyan ya samar da kudaden.

Bankin duniya ya yi amfani da jimillar kudade a Sudan da yawansu ya kai dala miliyan 130 wajen gudanar da ayyuka a fannonin ilmi, kiwon lafiya, aikin gona, hakar ma'adanai, sauyin yanayi, da aikin samar da zaman lafiya, da kuma harkokin gudanar da kudade a kasar.

A cewar wata kididdiga ta kasa da kasa, kimanin mutane miliyan 2.2 ne rikicin Sudan ya raba su da matsugunansu, kuma mutane dubu 147 daga cikinsu suna yankin gabashin Sudan ne a jahohi 3 da suka hada da Geddarif, Red Sea da Kassala.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China