Rabin kasashen Afrika sun bayyana rashin karfin kwarewa a cikin manufofinsu da suka shafi rage talauci, in ji bankin duniya a cikin wani rahoton da ya fitar a ranar Talata.
A cewar wani bincike na baya bayan nan na ingancin manufofi da hukumomin cikin gida wato (CPIA) da bankin duniya ya gudanar a shekarar 2015, a yankin kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, ya nuna kasashe 7 cikin 38 sun kyautata kwarewarsu a yayin da kasashe 12 suka ga matakinsu ya yi kasa.
Ko da yake wasu kasashe na samun ci gaba sosai, amma wasu dake samun goyon bayan kungiyar raya kasa da kasa wato IDA har yanzu suna fuskantar wani jinkiri na ingancin manufofinsu, in ji Albert Zeufack, masanin tattalin arziki a bankin duniya reshen Afrika, wajen gabatar da binciken CPIA a birnin Abidjan a ranar Talata.
A cewar mista Zeufack, ya kamata a dauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tattalin arziki da kasashen Afrika suke fuskanta.
A ganin bankin duniya, rashin karfin kwarewar kasashen Afrika ta fuskar mulki na gari na nuna cewa, wajibi ne a karfafa karfin hukumomin gwamnati, ta yadda za su rika gabatar bayani game da ayyukansu na ci gaban jama'a, tsaro da shari'a ga 'yan kasa. (Maman Ada)