Bankin duniya ya ba da rahoton bincike mai taken "matalauta a Afrika dake samun bunkasuwa", wanda ya gabatar da batun talaucin da Afrika ke fama da shi a lokacin da saurin bunkasuwar tattalin arzikinta ya kai kashi 4.5 cikin dari.
Rahoton ya ce, ko da yake Afrika ta samu bunkasuwa a fannonin kiwon lafiya, da samar da abubuwa masu gina jiki, da tarbiyya da kuma samar da iko da dai sauransu, amma bunkasuwar tattalin arzikinta ba ta inganta kyautatuwar zaman rayuwar jama'a sosai ba. Nahiyar Afrika nahiya ce kawai da ba ta cimma burin muradun karni na MDD ba tukuna, yawan mutane mafiya talauci a nahiyar ya wuce miliyan 330, wanda ya karu da kashi 18 cikin dari bisa na makamantan lokacin shekaru 90 na karnin da ya wuce.
Bugu da kari, rahoton ya ce, saurin karuwar yawan mutane da bambancin dake kasancewa a fannonin kabilu da sana'o'i da kuma wuraren da aka haifu su ne muhimman dalilan da suka haddasa karuwar tazarar dake tsakanin attajirai da matalauta.(Lami)