in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi farin ciki da zaben sabon shugaban kasa a Somaliya
2017-02-11 13:09:24 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana farin cikinsa, kan yadda aka kammala zaben shugaban kasa lami lafiya a kasar Somaliya, inda aka zabi tsohon firaministan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mohammed Abdullahi Mohammed a matsayin sabon shugaban kasar.

Wata sanarwa da Kwamitin ya fitar a jiya Jumma'a, ta bayyana gamsuwarsa kan ci gaban da kasar Somaliya ta samu a fannonin siyasa da tsaro, tun bayan shekarar 2012.

Haka kuma, kwamitin ya jaddada bukatar kare yanayin dimokuradiyya a kasar, inda ya bukaci zababben shugaban da ya tattauna da majalisar dokoki kasar don tabbatar da mutanen da za su zama ministoci, yana mai cewa, dole ne a yi komai a bayyane ba tare da rufa-rufa ba.

Ban da haka kuma, kwamitin sulhun ya yi kira ga zababben shugaban da gwamnatin kasar, su dauki matakan gaggawa, don tunkarar matsalar yunwa da ka iya abkuwa sakamakon fari, gami da kira ga bangarorin kasa da kasa da su kara bayar da tallafi ga kasar Somaliya.

Har ila yau, kwamitin sulhun ya bukaci gwamnatin kasar da ta yi kokarin karfafawa rundunar sojanta gwiwa, ta yadda za ta iya karbar nauyin kare jama'ar kasar daga hannun sojojin wanzar da zaman lafiya dake karkashin jagorancin MDD.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China