A yau Jumma'a ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, mutuwar mutane masu yawa, tare da jikkatar wasu da dama, sakamakon harin ta'addanci da aka yi a jihar Sindh dake kudancin kasar Pakistan, ta girgiza kasar Sin matuka. Ya ce kasar Sin ta yi matukar tir da wannan hari na ta'addanci.
Rundunar 'yan sandan jihar Sindh ta ce, an kai harin bam din kunar bakin waken ne a wani wurin addini a yankin Sehwan a daren ranar 16 ga wata, harin da ya haddasa mutuwar mutane 72, tare da raunatar mutane fiye da 200. (Tasallah Yuan)