Sakataren janar na MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a wani asibitin birnin Quetta dake kudu maso yammacin kasar Pakistan, tare da kimanta shi da wani hari mai munin gaske.
A ranar Litinin, a kalla mutane 70 suka mutu kana wasu 112 suka jikkata a cikin wani harin kunar bakin wake na bam a sashen ba da jinyar gaggawa na asibitin Quetta. Fashewar ta faru ne a lokacin da wani gungun lauyoyi suke rakiyar gawar wani abokin aikinsu, wani babban lauyan Balouchistan, Bilal Anwar Kasi, da aka kashe cikin wani hari.
Kai hari kan abokai da 'yan uwan wani mamaci a cikin asibiti, ya sanya wannan hari kasancewa mai munin gaske, in ji mataimakin kakakin MDD, Farhan Haq a yayin wani taron manema labarai. Sakataren janar na bukatar gwamnatin Pakistan da ta yi iyakacin kokari domin tabbatar da tsaron al'umma da kuma gurfanar da masu hannu kan wannan hari na yau, in ji mista Haq. Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan harin ta'addanci. (Maman Ada)