in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi hadarin jirgin sama a Pakistan
2016-12-08 11:06:22 cri
A yammacin jiya Laraba 7 ga wata, wani jirgin saman fasinja na kamfanin jirgin saman kasa da kasa na Pakistan (PIA) ya fadi a yankin Havelian dake arewacin kasar. Wani kakakin kamfanin PIA ya bayyana cewa, wannan jirgin sama dake dauke da mutane 48 baki daya, wadanda suka hada da ma'aikatan jirgin saman 5, fasinjoji 42 da kuma wani ma'aikacin filin jirgin sama.

Kafofin yada labarai na wurin sun ba da labarin cewa, rundunar soja ta riga ta samu akwatin nadar bayanai na jirgin saman. Kawo yanzu masu aikin ceto sun samu gawawwaki 36. Ana ganin, akwai wuya a sami wasu da su tsira da raykansu a wannan hadarin. Jirgin saman dai ya tashi daga Chitral dake arewa maso yammacin kasar zuwa Islamabad a yammacin jiya da misalin karfe 3 da minti 38. Bayan awa daya kawai, jirgin ya daina mu'amala tsakaninsa da filin jirgin saman.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China