in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 72 sun mutu a sakamakon harin kunar bakin wake a kudancin kasar Pakistan
2017-02-17 10:52:06 cri
Rundunar 'yan sandan jihar Sindh dake kudancin kasar Pakistan ta ce, an kai harin bam din kunar bakin wake a wani wurin addini a yankin jihar Sehwan a daren ranar 16 ga wata, harin da ya haddasa mutuwar mutane 72 tare da raunatar mutane fiye da 200.

An ruwaito wani jami'in kiwon lafiya a yankin Sehwan na cewa, mata da yara da dama na daga cikin mutanen da suka mutu. Kana an dauki mutane da dama da suka ji rauni zuwa Hyderabad da Karachi ta jirage masu saukar ungulu.

Wani babban jami'in 'yan sandan yankin Sehwan ya bayyana cewa, maharin ya shiga wurin Ibadar ne, inda nan take ya tayar da bam din da ke jikinsa. Bayanai na nuna cewa, akwai mutane 500 zuwa 800 a wurin Ibadar a lokacin bam din ya tashi. Yanzu haka 'yan sanda da dama ne suka yi wa wurin kawanya.

Daga bisani kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai harin.  (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China