Ministan sufurin kasar, Ali Ahmed Jama ne ya sanar da batun dakatar da zirga-zirgar jiragen ga kamfanonin shirya tafiye-tafiye.
Sai dai Ministan ya ce, matakin ba zai shafi sauran filayen jiragen saman kasar ba, tun da zaben zai gudana ne a babban birnin kasar kadai.
Har ila yau, za a rufe dukkan manyan titunan Mogadishu na tsawon kwanaki biyu, har sai an kammala zaben.
Magajin garin Mogadishu Yusuf Jimale ne ya sanya haramci zirga-zirga a kan titunan Mogadishu da nufin tabbatar da tsaro yayin zaben. (Fa'iza Mustapha)