Kwamitin na PEC mai kunshe da 'yan majalissun dokokin kasar na dattijai da wakilai su 18, ya ce shugaban kasar mai ci Hassan Sheikh Mohamud, da Firaministan kasar Omar Abdirashid Ali Sharmarke, tare da tsohon shugaban kasar Sharif Sheikh Ahmed, na cikin na gaba gaba a 'yan takarar.
Wasu daga 'yan takarar dai na da shaidun zama 'yan wata kasar ta daban baya ga kasar ta Somaliya, sai dai kwamitin na PEC ya ce hakan ba zai zamo wata matsala ba. Ko wane 'dan takara dai zai biya kudi har dalar Amurka 30,000, tare da wasu karin ka'idajojin shiga zaben.
Bisa tanajin tsarin mulkin kasar Somaliya, majalissun dokokin kasar biyu za su yi zama na hadin gwiwa, domin zabar wanda zai zamo sabon shugaban kasar, kuma wajibi ne wadanda zai lashe zaben ya samu adadin kuri'u da suka kai kaso 2 bisa 3 na jimillar kuri'un da za a kada. Adadin da zai kai kimanin kuri'un 'yan majalissa 219 ke nan. Gaza samun wannan kuri'u ga 'dan takara guda, zai sanya shiga zagaye na biyu na zaben, wanda zai kushi 'yan takara 4 mafiya samun kuri'u a zagayen farko. (Saminu)