Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya cinna wuta kan ton 15 na hauren giwa na sumogal, tare da yin alkawarin kara karfafa yaki da manyan laifuffukan dake kawo illa ga namun dajin kasar.
Mista Kenyatta ya kona wani tarin hauren giwa a gaban idon mambobin gwamnati, jakadun kasashen wajen dake kasar da wakilan kungiyoyin kare namun daji da muhallin halittu, a yayin bikin ranar namun daji ta duniya.
A tsawon shekaru uku da suka gabata, farautar namun daji ba bisa doka ba da kuma sumogal kayayyakin namun daji sun kasance babban kalubale ga kasar Kenya. Wadannan manyan laifuffuka na kawo barazana ga muhallin halittu, tsaro da zaman lafiya, in ji shugaba Kenyatta.
Kasar Kenya dake gabashin nahiyar Afrika ta kafa wasu tsare tsaren dokoki da kuma zuba jari kan kimiyyar zamani domin karfafa yaki da wadannan manyan laifuffuka dake kawo illa ga muhallin halittu, in ji shugaba Kenyatta, tare da ambato sanya hannu kan dokar kare muhallin halittu a shekarar 2013, da bullo da sabbin fasahohin zamani da kuma daukar jami'an tsaron daji dake sintiri domin yaki da farauta ba bisa da doka ba. (Maman Ada)