Ma'aikatar muhalli ta kasar Angola tana shirya wani jadawali na kasa da zai yaki fataucin hauren giwaye da ake yi ba bisa ka'ida ba a sherara ta 2015 zuwa ta 2017, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Angola ya ruwaito.
Jadawalin da aka shirya shi bisa dokar kasa da kasa na hana cinikin namun dajin dake fuskantar barazanar karewa, ya bukaci a karfafa bincike a filayen jiragen sama da kuma kan iyaka domin magance fataucin hauren.
Angola dai na daga cikin kasashe 3 a duniya da kasa da kasa ke damuwa a kai, ganin ta zama cibiyar safarar haramtattun hauren giwa ga sauran kasashe tare da Cambodia da kuma Laos.
Filipe Kodo, wani masani a ma'aikatar muhallin kasar ya ce, wannan fataucin hauren giwa ba da izini ba yana shafar kasashe da dama, kuma wassu kayayyakin daga sauran kasashe makwabta da ake shigowa da su ta kasarsu, a tsallaka da su zuwa kasuwannin wassu kasashen.
Angola na daga cikin kasashen 'yan kadan da ba su haramta cinikin hauren giwa da kayayyakin da ake samarwa daga jikin ba, wadanda ake sayarwa a ko ina a kasuwannin kudancin birnin Luanda.
Kasar a yanzu haka tana kokarin canza tsarin ne ta karfafa bincike da kafa dokoki, har ma da wayar da kan jama'a a kan daina cinikin hauren giwayen, in ji Filipe Kodo. (Fatimah)