Gwamnatin kasar Tanzaniya ta yi maraba da matakin da kasar Sin ta dauka na baya bayan nan game da haramta yin safarar hauren giwa, inda ta bayyana cewa, wannan mataki ya kasance abu mai matukar muhimmanci a tarihi wanda zai magance barazanar bacewar wannan dabba a doron kasa.
Ministan albarkatun kasa da yawon bude ido na kasar Jumanne Maghembe, ya ce wannan yunkuri zai rage yawan kudaden da kasashen Afrika ke kashewa wajen yaki da masu farautar giwaye.
A ranar 30 ga watan Disamba ne kasar Sin ta ayyana aniyarta ta daina ta'amalli da hauren giwa nan da karshen shekarar 2017.
Ministan ya ce, wannan ya bayyana a fili yadda kasar Sin take da aniyar kare dabbobi a nahiyar Afrika, kuma hakan ya sake tabbatar da irin abokantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)