Mr. Guterres wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, gaban mahalarta taron shugabannin kungiyar ta AU karo na 28 dake gudana a Addis Ababan kasar Habasha, ya ce MDD za ta hada gwiwa da AU wajen cimma muradun nahiyar Afirka, wadanda suka hada da wanzar da zaman lafiya da tsaro.
Ya ce yana farin cikin ganin yadda nahiyar ke tura tawagogin ta, domin aiki cikin rundunonin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa masu yawa, da ma karbar 'yan gudun hijira da nahiyar ke yi.
A daya bangaren kuma, babban magatakardar MDDr ya ce wasu kasashen nahiyar ta Afirka, na sahun gaba wajen samun ci gaba cikin sauri a duniya.