Mahamat ya yi nasarar lashe wannan mukami ne bayan da ya kayar da abokan takararsa hudu da suka fafata a neman wannan mukami. Wato ministocin harkokin wajen kasashen Botsawana Pelonomi Venson-Moitoi, na Equatorial Guinea Agapito Mba Mokuy, da ta Kenya Amina Mohammed da na Senegal Bathily Abduolaye kana manzon musamman na MDD mai kula da Afirka ta tsakiya.
A karon farko 'yan takarar guda biyar sai da suka gabatar da wata muhawara ta talabijin a watan Disamban da ya gabata a hedkwatar kungiyar ta AU da ke birnin Addis Ababan kasar Habasha gabanin wannan zabe.
Yanzu dai Mahamat zai maye gurbin Madam Nkosazana Dlimini Zuma 'yar kasar Afirka ta kudu, kana mace ta farko da aka zaba a wannan mukami a shekarar 2012.(Ibrahim)