Taron na 30 wanda kwamitin zartaswar kungiyar ya gabatar, ya gudana ne karkashin babban zama na 28, da ake sa ran shugabannin kasashe mambobin kungiyar za su gudanar nan da 'yan kwanaki.
Yayin taron, shugabar kwamitin zartaswar kungiyar uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta jaddada bukatar da ake da ita, ta kara dunkulewar Afirka, tare da bunkasa ci gaban nahiyar. Zuma ta kuma ja hankalin kasashe mambobin kungiyar, da su zage damtse wajen cimma nasarar kudurorin ci gaban nahiyar nan da shekarar 2063.
Har wa yau Dlamini-Zuma, ta jaddada bukatar fara aiwatar da manufar samar da yankin cinikayya maras shinge na nahiyar ko CFTA nan da karshen shekarar nan da muke ciki, da baiwa al'ummun nahiyar damar shiga kasashen juna, matakin da ta ce zai bude damammaki na cinikayya, da yada ilimi, tare da yawon bude ido a nahiyar.
Taron na wannan karo dai na zuwa ne, gabanin taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta AU karo na 28, wanda ke tafe tsakanin ranekun 30 zuwa 31 ga watan nan na Janairu. (Saminu)