Elham wadda ta bayyana hakan a jiya Juma'a, gabanin bude taro na 28, na jagororin kungiyar ta AU, ta kara da cewa tuni kungiyar ta cimma wasu tarin nasarori a shirye shiryen ta na bunkasa samar da makamashi, da harkar sufuri, da fasahar sadarwa, wadanda su ne manyan sassa da nahiyar ke matukar bukatar ingantar su.
Ta ce AU da hadin gwiwar abokan huldar ta, sun cimma nasarar share fagen amfani da makamashi mai tsafta a Afirka. Kaza lika kungiyar na aiwatar da wani shiri na musamman, na samarwa daukacin al'ummun nahiyar Afirka wutar lantarki ta hanyoyi na zamani, karkashin shirin cimma muradun nahiyar, nan da shekarar 2063.
Bugu da kari, Elham ta ce AU ta kaddamar da shirin samar da makamashi mai tsafta na Afirka ko AREI a takaice, a cikin watan Disambar shekarar 2015, shirin da ke da nufin cimma gajiyar makamashi mai tsafta, matakin da zai haifar da ci gaba mai dorewa ga nahiyar Afirka.