in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarayyar Afrika AU na sa ran biyan kudaden dukkan ayyukanta da kanta.
2017-01-28 12:59:22 cri
Mataimakin shugaban Tarayyar Afrika AU Erastus Mwencha, ya ce dukkan shugabannin kasashe mambobin kungiyar AU, sun amince su samar da kashi dari na kudaden da za su aiwatar da kasafin kudin kungiyar na shekaru biyar nan gaba.

Ya ce shugabannin kasashen sun amince cewa, cikin shekaru biyar masu zuwa, dole ne kungiyar ta yi kokarin samar da kashi dari na kudaden da za ta kasha, kashi 75 na gudanar da ayyuka, kashi 25 kuma na wanzar da tsaro a yankin.

Samar da kudaden aiwatar da ayyukan kungiyar matsaya ce da shugabannin kasashe mambobin kungiyar suka cimma, yayin wani taron kungiyar karo na 27 kan samarwa kungiyar kudade, da ya gudana a birnin Kigalin kasar Rwanda a watan Yulin 2016. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China