Kafofin watsa labaran kasar Rasha sun ce, daga cikin fasinjojin 84, akwai 'yan wasa 64 na shahararriyar kungiyar wasan kade-kade da raye-raye ta sojan Rasha, mai suna Alexandrov Ensemble, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa sansanin sojan saman Hmeymim na kasar Rasha dake kasar Siriya, don gabatar da wasannin murnar sabuwar shekara.
Daga cikin fasinjojin kuma, akwai shugaban sashin kula da al'adu na ma'aikatar tsaron Rasha, da babban jagoran kungiyar wasan kide-kide ta rundunar sojan Rasha, tare kuma da 'yan jaridun kasar guda 9.
A wani labarin kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da yau Litinin 26 ga wata, a matsayin ranar zaman makoki.
Haka kuma, ya ba da umurnin binciken musabbabin aukuwar hatsarin. (Murtala Zhang)