Ma Zhaoxu ya jaddada cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su ciyar da aikin tsara yarjejeniyar batun ci rani ta kasa da kasa gaba yadda ya kamata, haka kuma ya dace a nuna amincewa kan babbar gudummawar da 'yan cin rani suke bayarwa wajen raya tattalin arzikin kasa da kasa, yayin da kiyaye ikonsu yadda ya kamata, a sa'i daya kuma, ya kamata a mutunta manufofin kasa da kasa kan batun ci rani.
Haka zalika, Ma Zhaoxu ya yi kira ga kasashe masu ci gaba da su aiwatar da alkawarin da suka yi wa kasashe masu tasowa yadda ya kamata, ta yadda za su taimaka wa kasashe maso tasowa wajen neman bunkasuwa, haka kuma, ya kamata a ci gaba da kyautata ayyukan ci rani cikin kasa da kasa bisa fannoni daban daban. Sa'an nan kuma, Mr. Ma ya jaddada cewa, kasar Sin tana goyon bayan kungiyar 'yan ci rani ta kasa da kasa da ta karfafa ayyukanta na ba da jagoranci da shiga tsakani cikin harkokin cin rani na kasa da kasa, a sa'i daya kuma, ya kamata kasashen asali na 'yan ci rani da kuma kasashen da 'yan ci ranin suke son zama su dauki alhakinsu yadda ya kamata wajen kiyaye tsaron hanyoyin ci rani masu dacewa da dokoki, sannan a dauki matakai na yaki da laifufukan sata zuwa wata kasa da kuma safarar bil adama. (Maryam)