Masu aikin ceto sun tsamo gawawwakin mutane da dama, bayan da wani jirgin ruwa dauke da 'yan ci rani ya nutse a kusa da birnin Al-Qrbula, dake da nisan kilomita sama da 50 daga birnin Tripolin kasar Libya.
Wani jami'in rundunar sojin ruwan kasar ta Libya ya bayyana cewa, jirgin mai tsahon mita 8, na dauke ne da fasinjoji 130, ya kuma karye ne a ranar Lahadi, ana kuma tsammanin yana hanyarsa ne ta tsallakawa da 'yan ci ranin zuwa kasar Italiya. Baya ga wadanda suka rasu, a cewar wannan jami'i, ma'aikatan ceto sun samu damar kubutar da mutane 45.
Kasar Libya dai ta dade da kasancewa hanya mafi sauki da 'yan ci rani ke bi, wajen shiga kasashen Malta da Italiya, dama sauran kasashen Turai, sakamakon raunin tsaron kan iyakokinta.
Bugu da kari, gwamnatin kasar ta rikon kwarya ta gaza samar da tsaron kan iyakokin kasar, tun bayan hargitsin da ya janyo kifar da gwamnatin shugaba Muammar Gaddafi a shekarar 2011 da ta gabata, lamarin da ya kara habaka safarar 'yan ci rani daga yankunan arewacin Afirka ta sassan ruwan kasar zuwa kasashen Turai. (Saminu)