Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana bukatar zage-damtse wajen gudanar da aikin ceton 'yan ci ranin da hadarin jirgin ruwa ya rutsa da su a tekun Mediterranean.
Mr. Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a jiya Lahadi, ya ce, ya kadu da jin rasuwar mutane kusan 700, sakamakon nutsewar wani jirgin ruwa mai dauke da 'yan ci rani, da masu gudun hijira a gabar tekun Libiya.
A baya bayan nan dai ana yawan samun aukuwar hadurran jiragen ruwa, wadanda ke safarar baki 'yan ci rani daga arewacin Afirka zuwa nahiyar Turai. An ce, hadarin na daren ranar Asabar ya auku ne daura da kudancin yankin Sicily na kasar Italiya.
Hukumar lura da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta ce, cikin sama da mutane 700 dake cikin jirgin ruwan, an samu nasarar ceto kusan mutane 50.
A wannan shekara kadai, an kiyasta cewa, yawan masu kokarin tsallakawa Turai da suka rasa rayukansu, sun doshi mutane 1,500, matakin da ya sanya kasashen Turai daukar karin hanyoyin tsaron kan iyakokinsu, domin dakile kwararar bakin-haure, duk kuwa da suka da wannan mataki ke sha daga kungiyoyin ba da agajin jin kai.
A bara kadai, kididdiga ta nuna cewa, a kalla mutane 218,000 ne suka yi yunkurin tsallaka tekun Mediterranean zuwa kasashe daban daban dake tarayyar Turai, ciki hadda kusan mutane 3,500 da suka rasa rayukansu a kan teku. Wanda hakan ya sanya wannan yankin teku kasancewa hanya mafi hadari da 'yan ci rani ke bi zuwa Turai. (Saminu)