Rundunar sojojin Aljeriya da na Nijar suna cigaba da kokarinsu tun ranar Lahadin da ta gabata wajen gano 'yan ci rani kusan hamsin da masu kokarin ketara wa da su suka bari a cikin kunkurmin hamadar Sahara dake iyaka da kasashen biyu, in ji wata majiya mai tushe da ta fito daga jami'an tsaron kasar Aljeriya da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito a ranar Laraba.
Hukumomin kasar Nijar ne, a cewar wannan majiya, suka sanar da takwarorinsu na kasar Aljeriya da bacewar wasu mutane kusan hamsin dake kokarin ketare wa zuwa Aljeriya da yawancinsu mata da yara.
Rundunar sojojin Aljeriya na take tattara jami'anta, musamman ma sojojin sama, domin fadada ayyukan neman wadannan bayun Allah, in ji wannan majiya, tare da kara da bayyana cewa, aike yiyuwar wadannan 'yan ci rani ba su samu damar isa cikin kasar Aljeriya ba, kana kuma akwai wuyar a same su da rai, ganin mawuyancin yananin wannan wuri da ya hada da tsananin zafi, iska, musamman ma da kasa dake bayyana halin hamadar Sahara a wannan lokaci.
A farkon watan Oktoban shekarar 2013, 'yan ci rani fiye 90 suka mutu a lokacin da suka kokarin kaiwa shiga Aljeriya, a cewar hukumomin kasar Nijar. (Maman Ada)