in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya murnar kaddamar da taron tattaunawa kan cika shekaru 30 da zartas da sanarwar hakkin samun bunkasuwa
2016-12-04 17:32:03 cri
A yau Lahadi 4 ga wata, an kaddamar da taron tattaunawa na kasa da kasa kan cika shekaru 30 da zartas da sanarwar hakkin samun bunkasuwa a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da wasikar taya murnar bude taron, inda ya jaddada cewa, samun bunkasuwa muhimmin batu ne a cikin zamantakewar dan Adam, yana fatan kasa da kasa za su yi amfani da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030 ta MDD, tare da kama hanya mai adalci da bude kofa da kirkire-kirkire dake shafar dukkan fannoni don cimma burin samun bunkasuwa tare a kasa da kasa.

Xi Jinping ya jaddada cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya dake da mutane fiye da biliyan 1 da miliyan 300, samun bunkasuwa muhimmin batu ne da zai warware dukkan matsalolin da kasar Sin ke fuskanta, kana shi ne batu dake gaban kome yayin da jam'iyyar kwaminis ta Sin take gudanar da harkokin mulki a kasar Sin. Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar hada ka'idar baiwa dukkan dan Adam hakkinsa da yanayin da ake ciki a kasar, da maida hakkin rayuwa da samun bunkasuwa a matsayin hakkin dake gaban kome ga dan Adam. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China